Rundunar ƴan sandan Kano ta warware takaddama tsakanin Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH da KEDCO
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya bayyana cewa an warware matsalar da ta shafi katsewar wutar lantarki a cibiyar,
Bayan tattaunawa da Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) tare da shiga tsakani na Kwamishinan ƴan sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.
Bayan cimma matsaya, Shugaban KEDCO, Dr. Abubakar Shuaibu Jimeta, ya umurci injiniyoyinsa da su gaggauta mayar da wutar lantarki ga asibitin.
Hukumar AKTH ta gode wa kwamishinan ƴan sanda da kuma shugaban KEDCO bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin an kawo ƙarshen wannan matsala cikin lokaci.
Haka kuma, asibitin ya sake tabbatar da aniyar sa ta biyan dukkan bashin wutar lantarki da ake bin shi nan gaba.
Hukumar ta kuma mika godiyarta ga al’umma bisa hakuri da fahimtar da suka nuna, tare da jaddada cewa lafiyar marasa lafiya da ci gaba da ba da hidimar lafiya su ne babban abin da asibitin ke mayar da hankali a kai.