Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanar da cewa za a saka harajin kashi 100 cikin 100 kan duk wani fim da aka yi a wajen kasar.
A wani rubutu da ya wallafa a Truth Social a ranar Litinin, Trump ya ce matakin na da nufin dakile abin da ya kira da “sata” ta masana’antar fina-finan Amurka da kasashen waje ke yi.
Sai dai bai fayyace lokacin da matakin zai fara aiki ba, ko kuma yadda za a aiwatar da shi.
Wannan shi ne karo na biyu da ya yi irin wannan sanarwa. A watan Mayu, Trump ya sanar da irin wannan haraji kan fina-finan kasashen waje, inda ya danganta hakan da raguwar cigaban Hollywood sakamakon jan hankalin masu shiryawa da daraktoci zuwa kasashen waje saboda rangwame da ake basu.
Ya bayyana wannan yanayi a matsayin barazana ga tsaron kasa, tare da jaddada cewa wannan doka za ta “tsare” masana’antar fina-finan Amurka.
Trump ya Æ™ara da cewa ya bai wa ma’aikatar kasuwanci izini da ta fara aikin aiwatar da shirin, duk da cewa har yanzu cikakkun bayanai ba su fito ba.
Haka kuma ba a tabbatar ko sanarwar da aka yi a ranar Litinin na nufin ƙara wa harajin da aka sanar a baya bane ko kuma maimaita sanarwar ne kawai.