Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke Faretin bikin ranar samun ƴancinkai
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, inda aka bayyana cewa duk da soke faretin, hakan ba zai rage armashi ko muhimmancin ranar ba.
Sai dai sanarwar bata fayyace dalilin sokewar ba, lamarin da ke barin tambayoyi a zukatan al’umma, kasancewar faretin na ɗaya daga cikin manyan al’adu na bikin tunawa da ranar 1 ga Oktoba, 1960 ranar da Najeriya ta samu cikakken ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.