Jami'in Dan sanda ya yi kuskuren harbe kansa da Bindinga a Jihar Kano
Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa ransa sakamakon harbin kansa da bindiga da yayi bisa kuskure a bakin aiki a jihar Kano.
A cewar kafar yada labarai ta Zagazola Makama da ke bibiyar harkokin tsaro, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:40 na safiyar ranar Asabar a unguwar Hotoro.
Rahotanni sun ce jami’in da ke aiki a rundunar Æ´ansandan jihar Kano, ya shiga bandaki a harabar Kamfanin Basnaj Global Resources Limited, lokacin da bindigarsa ta harba.
Binciken farko ya nuna cewa Ibrahim ya harbe kansa a ciki yayin da yake tsugunawa da bindigarsa kirar AK-47 da ke rataye a wuyansa.
Bindigar mai lambar rajista GT 4177, an same ta tare da harsashi guda daya da ya harba, yayin da aka lissafa harsasai 29 daga cikin 30 da aka ba shi a farko.
An garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa, sannan aka kai gawarsa dakin ajiye gawa domin yi masa gwajin gano musabbabin mutuwa wato autopsy.