Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Laraba 1-10-2025 a matsayin ranar hutun cikar Najeriya Shekaru 65 da samun ƴancin kai
Gwamnatin tarayya ta sanar da Laraba, 1 ga Oktoba, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ƴancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya kuma taya ƴan Najeriya murnar wannan rana mai tarihi, yana mai kira da a ci gaba da zama masu kishin ƙasa da haɗin kai domin ci gaban al’umma.