Daga Hafsat Muhammad Abuja
Gwamnatin tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe (Project) a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yiwa kasa hidima (NYSC).
Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar.
Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka yi karatu.
Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin ta yi wanda ya alaƙanta aikin yiwa ƙasa hidima (NYSC) da tsarin tattara bayan ilimi na kasa (NERD).
Saboda haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba.
Gwamnatin tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi da bincike.