Yadda mutane da yawa suka mutu a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano AKTH saboda rashin wutar lantarki
Hukumomin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) sun yi kira ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Kano (KEDCO) da su gaggauta maido da wutar lantarki a Asibitin sakamakon mutuwar wasu majinyata a sashen agajin gaggawa.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar sashen yada labarai ta asibitin, Hauwa Inuwa Dutse, ta nuna matukar damuwarta kan lamarin,
Inda ta nuna cewa da a ce an ci gaba da samar da wutar lantarki za a iya dakile asarar rayuka.
Sanarwar ta ce, AKTH na biyan kudin wutar lantarki a kai a kai daga cikin kudaden shigarta na cikin gida (IGR) yayin da ta kuma kashe makudan kudade wajen sayo man dizal ga janaretonta domin kara samar da wutar lantarki.