Ana zargin sace wayar hannu ta Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Barista Sule Shu’aibu (SAN).
Lamarin ya faru ne a lokacin wani taron da ya shafi harkokin tsaro da aka gudanar a Kaduna a yai Alhamis.
Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa satar ta faru ne a bainar jama’a, abin da ya haifar da tambayoyi kan yadda mai laifin ya samu damar aikata hakan a wurin da ke cike da jami’an tsaro.
Jaridar ta rawaito cewa har zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoto, ba a kama wanda ake zargi da laifin ba, kuma hukumomin jihar Kaduna ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma game da lamarin ba.