A yau ne aka gudanar da bikin kaddamar da sabon shugabanci na gidauniyar A
lkhairat Aid Foundation for Community Development, wata kungiya mai zaman kanta da ke gudanar da ayyukan ci gaban al’umma tare da tallafawa mabukata a fannoni daban–daban.
lkhairat Aid Foundation for Community Development, wata kungiya mai zaman kanta da ke gudanar da ayyukan ci gaban al’umma tare da tallafawa mabukata a fannoni daban–daban.
A sabon jagorancin da aka sanar, Hajiya Ummulkhairi Mukhtar ce ta karɓi matsayi na Director General (DG), yayin da Hajiya Hadiza ta kasance Deputy Director. Sauran manyan mukamai sun hada da:
Hajiya Amina Muhammad – Secretary General
Comr Buhari Gambo – Assistant Secretary General
Hajiya Humaira Muttaka – Executive Member
Da sauran su.
A cikin jawabanta bayan karɓar aiki, Hajiya Ummulkhairi ta gode wa mambobin gidauniyar bisa amincewa da basu wannan amanar, tare da alkawarin gudanar da aiki cikin gaskiya, hadin kai da manufa ta taimakon al’umma, musamman a bangaren ilimi, lafiya, jin kai da habaka matasa.
Kungiyar ta yi kira ga al’umma, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki da su mara musu baya don cimma burinsu na kawo ci gaba mai dorewa ga al’umma.
