Kotu ta sake umarni a kama Basarake Sadiq Ismaila Talban Warawa
Babbar Kotun Jihar Kano da ke zamanta a Miller Road karkashin jagorancin Mai Shari’a Hafsat Yahaya Sani ta jaddada umarnin da ta bai wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano da ya kama Basaraken Warawa, Alhaji Sadiq Ismaila Talban Warawa, wanda ake zarginsa da aikata fyade ga yar aikin gidansa a unguwar Tudun Yola, cikin karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.
Kotun ta dage cewa dole a tabbatar da aiwatar da wannan umarni ba tare da bata lokaci ba domin cigaba da bin diddigin shari’ar da ke gabansa. Ana ci gaba da sauraren shari’ar, yayin da ake jiran cikakken rahoto daga hukumar ‘yan sanda kan matakan da aka dauka.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce da fargaba a tsakanin al’umma kasancewar nau’in laifin ya shafi cin zarafin mata da karya ‘yancin dan Adam. Ana ci gaba da jiran matakin da hukumomi za su dauka a kan wannan batu.
