Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 12:10 na rana, a ranar 17 ga Janairu, 20256, kan wani mummunan hari da aka kai gidan Haruna Bashir da ke unguwar Dorayi Chiranchi a cikin birnin Kano.
Rahotonni sun bayyana cewa wasu batagari da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan tare da kai wa matar gidan mai suna Fatima Abubakar mai shekaru 35 da ‘ya’yanta guda shida hari da muggan makamai. Wakilin mu Jameel Lawan Yakasai ya rawaiyo mana cewa ,
Sakamakon harin, dukkan wadanda abin ya shafa sun samu munanan raunuka da suka yi sanadin rasuwarsu.
Da samun labarin, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya gaggauta tura tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da ayyuka, DCP Lawal Isah Mani, zuwa wajen da lamarin ya faru.
An kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Hakazalika, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya umarci tawagar bincike karkashin jagorancin ACP Wada Jarma, Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID), da su gudanar da cikakken bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su gaban shari’a.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano na mika ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, al’ummar Dorayi Chiranchi, da daukacin al’ummar Jihar Kano bisa wannan mummunan lamari.