Allah ya yiwa fitaccen dan Kasuwa a Kano Alhaji Bature Abdulaziz rasuwa
Marigayin Alhaji Bature Abdulaziz ya kasance fitaccen bawan Allah, mai kyakkyawar mu’amala da jama’a, wanda ya bayar da gudunmawa mai yawa a rayuwarsa, musamman a fannonin da suka shafi al’umma da ci gaban jama’a.
Wannan rasuwa ta jefa iyalai, abokai da al’umma cikin jimami da alhini. Na cikin Kano da makwabtanta.
Muna roÆ™on Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jiÆ™ansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma ba iyalansa, ‘yan uwa da masoya haÆ™uri da juriyar wannan babban rashi.