Cikin Daren ranar Asabar da misalin karfe 02:00 Jami'an ƴan sandan Kano suka sami nasarar kama matashi Umar tare da abokin aikata kisan gillar sa.
Wanda yanzu haka yake hannun babbar hedkwatar ƴan sanda ta Kano Bompai, domin zurfafa bincike.
Har ila yau Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin kula da lafiyar Mallam Haruna, mijin matar da aka yi wa kisan gilla tare da ƴaƴanta 6, a gidan Kwari da ke yankin Chiranci a ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano.
Mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara a kan harkokin Tsangayu, Gwani Musa Hamza Falaki, ne ya bayyanawa manema labarai , hakan a ranar Lahadi 18 ga Janairu, 2026, biyo bayan da su ka ziyarci gidan da lamarin ya faru inda su ka tarar mutumin bashi da lafiya kuma aka wuce da shi asibiti.
Ya ce da su ka je gidan sun tarar mijin marigayiyar baya cikin hayyacinsa, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti, kuma gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da lafiyar sa, domin ceto rayuwar sa.
Ya ce tuni gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin a zurfafa bincike domin kamowa, tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan duk wanda aka samu da laifi a kan aikata ta'addancin ga mutanen.