Rashin Imani: yadda aka yiwa Mahaifiya da ƴa ƴanta 6 kisan gila harcikin gida a Kano
Nazauna Unguwar Chiranci dake yankin karamar hukumar kumbotso sun tsinci kansu cikin firgici, bisa samun kisan gila da akaiwa wata Mata da ƴa ƴanta su shidade.
Lamarin daya San jama'ar Kano cikin yanayi na tashin hankali, cikin yaran da aka kashe angano anyi amfani da keken dinki wajen bugawa wani yaro daga ciki, wanda kwakwalwarsa ta fito.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai Fatima Abubakar, matar gidan, tare da ’ya’yanta shida:
• Maimuna Haruna (shekaru 17)
• Aisha Haruna (shekaru 16)
• Bashir Haruna (shekaru 13)
• Abubakar Haruna (shekaru 10)
• Faruk Haruna (shekaru 7)
• Abdussalam Haruna (shekara 1 da rabi)
Dukkan su sun rasu a wannan mummunan lamari, yayin da har zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana gano waɗanda ake zargi da aikata kisan ba.
Hukumomin tsaro na ci gaba da bincike, yayin da al’umma ke kira da a gaggauta gano gaskiya da kawo ƙarshen irin wannan ta’asa.
Hakan yasanya al'amura suntsaya a wannan yankin, bisa jimami da fargabar rashin tausayi na wannan kisa.