Daga Mutawakkilu Ibrahim Idris
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida), ya amince da bai wa hukumomi biyu da ke ƙarƙashin Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida damar ɗaukar sababbin ma'aikatan dindindin domin ƙarfafa ayyukansu da inganta hidimar gwamnati.
Daga cikin hukumomin da suka samu wannan amincewa har da Hukumar Tace Fina-finai da Dab'i ta Jihar Kano, wadda ta shafe fiye da shekara 16 ba tare da samun izinin ɗaukar sababbin ma'aikata ba. Bayanai sun nuna cewa tun daga shekarar 2010 ba a sake sahale wa hukumar ɗaukar ma'aikatan dindindin ba, lamarin da ya haifar da ƙarancin ma'aikata tare da ƙara nauyin aiki.
A cewar majiyoyi daga ma'aikatar, wannan mataki na gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya nuna jajircewarta wajen farfaɗo da hukumomin gwamnati da kuma tabbatar da cewa suna da isassun ƙwararrun ma'aikata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
An bayyana cewa ɗaukar sabbin ma'aikatan zai taimaka wajen inganta sa ido kan harkokin fina-finai da wallafe-wallafe, da kuma ƙara ingancin ayyukan da hukumar ke gudanarwa a faɗin jihar.
Masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai sun yabawa gwamnatin jihar bisa wannan mataki, suna mai cewa zai ba matasa masu ƙwarewa damar samun aikin yi tare da ƙarfafa hukumomin gwamnati wajen cika nauyin da doka ta ɗora musu.
Ana sa ran hukumomin da abin ya shafa za su bayyana cikakken tsarin ɗaukar ma'aikatan, tare da ƙa'idoji da sharuɗɗan neman aikin, bayan kammala shirye-shiryen gudanar da aikin ɗaukar ma'aikatan.
