‘YAN SANDA SUN GUDANAR DA CI GABA DA SAMAME DA KAWAR DA MABOYAR ‘YAN TA’ADDA A DAJIN GWAMNA, DAJIN GOMO HAR ZUWA DAJIN FALGORE
A wani sabon yunkuri na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Jihar Kano, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gudanar da gagarumin samame na kakkabe miyagun ayyuka a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamba, 2026, a Dajin Gwamna da Dajin Gomo, har zuwa Dajin Falgore, wanda ke makwabtaka da Jihar Bauchi.
Wannan samame na daga cikin dabarun da rundunar ke amfani da su wajen dakile ayyukan bata-gari, fatattakar masu aikata laifuka daga maboyarsu, tabbatar da tsaron hanyoyin daji da kuma kare rayukan al’umma, manoma, ‘yan kasuwa da matafiya, musamman a wannan lokaci na watannin karshen shekara.
Manufar wannan aiki ita ce fatattakar miyagun mutane da ke fakewa a dazuzzuka, rusa sansanoninsu da maboyarsu idan akwai, tare da tabbatar da tsaron jama’a da masu zirga-zirga a kan hanyar Kano zuwa Bauchi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, wanda shi ne ya jagoranci kuma ya sa ido kan wannan aiki, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da wannan kokari domin tabbatar da tsaro a jihar. Ya jaddada cewa aikin zai ci gaba ba tare da gajiyawa ba, har sai an kawar da dukkan maboyar masu aikata laifuka a cikin jihar da kewayenta.
Kwamishinan ya kuma tabbatar wa al'ummar Kano cewa rundunar ta dukufa wajen tabbatar da tsaro a wannan lokaci na karshen shekara, kasancewar watannin karshen shekara na zuwa ne da karuwar harkokin kasuwanci, zirga-zirgar ababen hawa da bukukuwa.
Haka kuma, ya bayyana cewa wadannan ayyuka na ci gaba da gudana ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin babban z