’YAN SANDA SUN KAMA SHAHARRAREN DAN DABA 'TA’AMBO' A RIMIN KEBE
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da kama wani fitaccen dan daba mai suna Umar Usman, wanda aka fi sani da Ta’ambo, mai shekaru 25, a unguwar Rimin Kebe.
An kama wanda ake zargin ne a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, da misalin karfe 8:40 na dare, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma sa ido na tsawon makonni.
Ana zargin Ta’ambo da jagorantar ayyukan daba, fashi da kwacen wayoyin hannu da sauran kayayyaki a Rimin Kebe, yankin Ramin Research da kusa da Asibitin Galula.
Haka kuma, ana zarginsa da kai hare-hare da jikkata jami’an tsaro.
A halin yanzu, wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda, inda ake gudanar da bincike.
Rundunar ta kuma ce tana kokarin cafke sauran ’yan kungiyarsa da kuma kwato kayayyakin da aka sace.