Akalla mutane 13 ne rahotanni su ka ce an kashe inda aka yi garkuwa da wasu da dama a wani sabon hari da ƴan bindiga su ka kai a kauyen Atak’Njei da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Jaridar News Point Nigeria ta bayar da rahoton cewa, harin na jiya na zuwa ne makonni kadan bayan wani lamari makamancin haka ya lashe rayukan mutane goma a yankin Langson da ke karamar hukumar.
A cewar jaridar, har yanzu dai hukumomin ƴansanda ba su ce uffan ba kan lamarin, amma shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Atyap, Sam Timbuwak ya shaida wa News Point Nigeria ta wayar tarho cewa ƴan bindigar sun mamaye garuruwan ne daga wani daji da ke kusa da wajen da misalin karfe 11 na daren Laraba, inda suka fara harbe-harbe a gidajen mutane.
Ya ce ƴan bindigar sun kai hari sama da gidaje 15, inda suka harbe mutane 13 ciki har da kananan yara har lahira, sannan su ka yi awon gaba da wasu matasa ‘yan mata yayin da wasu hudu suka samu raunuka daban-daban.
Shugaban na Atyap wanda ya bayyana cewa wurin da aka kai harin yana kusa da wani shingen binciken sojoji, sai dai ya koka kan yadda sojoji suka makare zuwa cikin al'umma bayan da maharan suka aikata munanan laifuka kuma suka tafi.
Lokacin da News Point Nigeria ta tuntubi kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce yana sane da faruwar lamarin kuma ya yi alkawarin baiwa wannan jarida da karin bayani.