“A jihar Edo, kimanin maniyyata 350 ne suka biya kuɗin aikin Hajjin bana gaba daya ko kuma wani bangare,” in ji Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Edo, Sheikh Ibrahim Oyarekhua.
Ya ce hukumar na son adadin ya kai na maniyyata 400, inda ya ƙara da cewa, “Mun nemi karin gurbi guda 150, kuma a taron gaggawar da muka yi, mun gabatar da bukatar a hukumance ga shugaban NAHCON, kuma ya yi mana alkawarin zai duba wannan bukatar ta mu,”
Ibrahim Oyarekhua ya bukaci maniyyatan da suka riga su ka biya wani kaso na kudaden da su yi maza su cika a kan lokacin da aka kayyade domin su samu damar tafiya zuwa kasa mai tsarki.
Hakazalika, babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna, Dakta Yusuf Yaqubu Alrigasiyu, ya bayyana cewa hukumar za ta bukaci karin kujeru 500 na aikin hajjin bana.
Ya ce bukatar hakan ita ce ta baiwa sauran maniyyatan da ake sa ran za su biya kudin kujeru a jihar nan da kwanaki masu zuwa.
Dokta Alrigasiyu ya bayyana cewa tuni Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta ware wa jihar kujeru dubu 5,987, inda ake sa ran maniyyatan za su biya Naira miliyan 2.919 kan ko wacce kujera a wata ganawa da manema labarai da ya yi a ranar Talata.