Shugaban kasar China, Xi Jinping, firaministan Burtaniya Rishi Sunak, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na daga cikin shugabannin kasashen duniya da tuni su ka aike da sakon fatan alheri ga Tinubu.
Wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na zababben shugaban kasar ya fitar a jiya Laraba, ta ce shugaba Erdoğan, wanda ya bayyana Tinubu a matsayin ɗan uwa, ya bukaci hadin kai da hadin gwiwa da zai kara dankon zumunci tsakanin Turkiyya da Nijeriya.
Erdoğan, a cikin wasikar ta sa, ya kuma jaddada muhimmancin Nijeriya a matsayin “kasa mafi karfi a Nahiyar Afrika” tare da yi wa Asiwaju Tinubu fatan samun nasarar gudanar da mulki wanda zai kawo ci gaba ga al’ummar Nijeriya.
Shugaba Erdoğan ya rubuta cewa: “A madadin al’ummar Turkiyya da na kaina, ina mika sakon taya murna ga mai girma bisa zaben da aka yi maka a matsayin shugaban Tarayyar Najeriya a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023. .
“Na yi imanin cewa, a matsayina na abokiyar huldar mu, Nijeriya, a karkashin jagorancin ku, za ta ci gaba da tafiyar da harkokinta zuwa makoma mai albarka. Turkiyya ta dauki inganta dangantakarta da Najeriya, a matsayin kasa mafi karfi a nahiyar Afirka da muhimmanci sosai.