Kakakin jam'iyyar ta NNPP ya shaida mana faruwar al'amarin inda yace: ƴan takara su tara da suka fafata a zaben ‘yan majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan a karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, sun kalubalanci babbar abokiyar hamayyarsu ta APC da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, a gaban kotu.
Ƴan takarar jam’iyyar NNPP sun shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano da na ‘yan majalisar dokoki ta kasa da ta jiha da ke zaman harabar kotun Miller.
Masu shigar da kara sun kuma roki kotun da ta amince da bukatarsu ta neman a shigar da kara.
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta gabatar musu da bukatar da ta ba su damar duba kayayyakin da INEC ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga Maris 2023.
Bukatar tasu ta kuma yi iyaka da neman izinin kotu don cigaba da gudanar da zaben, tare da cika dukkan matakan da suka wajaba na kotu dangane da bibiyar lamarinsu.
Haka kuma, jiga-jigan jam’iyyar NNPP sun gurfana a gaban kotu domin kalubalantar batutuwan da suke ganin sun sabawa tanadin dokar zabe ta 2022.
Ƴan takarar jam’iyyar NNPP da suka tayar da karar INEC da APC sun hada da Aminu Saidu Ungogo, Isiyiaku Ali Danja, Abdullahi Ali. Manajan Wudil, Kabiru Getso Haruna, Mahmud Tajo Gaya, Abdullahi Iliyasu, Musa Adamu Ahmad, Aminu Ibrahim Dambatta, Abdu Ibrahim Madaris.
An shigar da karar ne a gaban kotu a ranar 4 ga Afrilu, 2023.