A yau Alhamis, 13 ga watan Afrilu ne Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ke cika shekara 16 da rasuwa.
Jaridar Raihana ta tuna cewa an harbe fitaccen malamin addinin Musuluncin ne yayin da ya ke jan sallar Asuba a masallacin Almundata da ke unguwar Dorayi a Jihar Kano.
Kisan gillar da aka yi wa Shehin malamin ya faru ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Afrilun 2007.
Mu na addu'ar Allah Ya karɓi shahadar Mallam, Ya sa yana cikin rahma, ameen.