Ƙungiyar ta ɗauki matakin dakatar da Mane, ɗan ƙasar Senegal ne biyo bayan hatsaniya da ta haɗa shi da abokin taka ledar sa, Leroy Sane, ɗan ƙasar Jamus, jim kaɗan bayan wasan da Manchester City ta lallasa su 3-0 a gasar zakarun Nahiyar Turai a ranar Talata.
Jaridar Raihana ta rawaito cewa a ƙarshen wasan ne ƴan wasan biyu da su ke takawa Munchen leda su ka samu hatsaniya, inda rigimar ta yi ƙamari bayan an tashi daga wasan, har ta kai ga Mane ya nuna halin shago, inda ya naushi Sane a fuska, har ta kai ga ya ji masa ciwo.
Wannan ne ya sanya ƙungiyar ta kafa kwamitin ladabtar wa, inda ya yanke hukuncin dakatar da Mane, wanda ya lashe gasar zakaran ƴan wasan Afirka na 2022, was ɗaya.
Hukuncin na nufin cewa Mane ba zai buga wasa da kungiyar za ta kara da Hoffeinheim a gasar Bundesliga na ƙarshen mako ba.