Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, tayi watsi da sanarwar da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Hudu Yunus, yayi na bayyana Aishatu Dahiru Binani ta jam'iyyar APC a matsayin wacce tayi nasara a zaɓen cike gurbi a gwamnan Adamawa, inda tace an sanar da sakamakon a lokacin da ba'a kammala tattara Kuri'u ba.
Cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafin ta na Tuwita, tace kwamishinan zaɓen ya shiga aikin Baturen zaɓen da aka turo jihar, saboda haka ta dakatar da cigaba da bayyana sakamakon, ta na kuma gayyatar su day dukkan masu ruwa da tsaki cewa su hallara a babbar hedikwatar hukumar dake babban birnin tarayya Abuja.