Uba, wanda ya yi kiran a jiya Litinin yayin raba abinci ga mabukata don buɗe-baki a watan Ramadan a Abuja, ya kuma yi kira ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, da ya yi iyakacin kokarinsa domin hada kan yan Nijeriya ba tare da la’akari da kabila, addini ko karkata ga siyasa ba.
Ya ce kiran ya zama wajibi domin samar da kasa mai zaman lafiya da ci gaba domin amfanin kowa.
“Ina taya Musulman Najeriya murnar zagayowar watan Ramadan na wannan shekara. Mu yi tunani tare da kwaikwayon kyawawan halaye na soyayya, bayarwa da sadaukarwa kamar yadda ake samu a cikin watan Ramadan.
“Ta yin hakan ne za a samu zaman lafiya da kaunar juna wanda hakan zai sa Najeriya ta samu zaman lafiya don samun ci gaba ta kowane fanni,” in ji shi.