Rashin baiwa Amaeci kyautar bikin ranar haihuwarsa na ɗaya daga cikin laifuka na a NPA -- Hadiza Bala
Tsohuwar shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA, Hadiza Bala Usman, ta ce ɗaya daga cikin dalilan da ya sa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya riƙa gallaza mata shi ne rashin ba shi kyautar murnar zagayowar ranar haihuwa.
Ta bayyana hakan ne a cikin sabon littafinta da ta saki a yauTalata, mai suna “Stepping on Toes: My Odyssey at the Nigerian Ports Authority”.
Tsohuwar shugabar ta NPA ta rubuta cewa manya a Najeriya da dama sun gana da ministan domin sasanta rikicin da ke tsakaninsu jim kadan bayan an nemi ta “ta ajiye muƙamin nata” a watan Mayun 2021.
A cewarta, minista ya ki amincewa da rokon da gwamnoni, shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali da sauran su su ka yi na a maido da ita bakin aiki, saboda wasu uzuri na son kai da rashin yi masa komai.
“Lokacin da gwamnonin su ka jajirce, sai ya shaida musu cewa yanzu bashi da ra'ayin tattauna maganar, kuma za su iya tuntubar shugaban ma’aikatan tarayya.
“Ya gaya ma wani da ya yi kokarin shiga tsakani cewa ni mai son kai ce kuma ban yi masa komai daga NPA ba har ma ban taba ba shi kyauta a bikin tunawa da ranar haihuwar sa ba!
"Shugaban hukumar kwastam ta Najeriya, Kanal Hameed Ali (Rtd) shi ma ya yi kokarin warware matsalar ta hanyar shiga tsakani a matakai daban-daban amma abin ya ci tura."