Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta bayyana damuwarta kan rigingimun da ake samu a jihohin Bayelsa da Kogi da jihar Imo gabanin zaɓen gwamnonin jihohin da ke tafe cikin watan Nuwamba.
Shugaban hukumar zaɓen farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin taron kwamitin tuntuɓa kan sha'anin tsaro na hukumar da aka gudanar a babban ɗakin taro na hukumar da ke Abuja.
Farfesa Mahmood ya ce ''a yayin da muke nazari kan baban zaɓen ƙasar da ya gabata, yana da kyau mu mayar da hankali kan zaɓen gwamnoni da ke tafe a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi''.
Tuni dai aka ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohin uku daga ranar 14 ga watan Yuli, za kuma a ci gaba har zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Hukumar zaɓen ta ce tuni aka fara samun alamomin tashe-tashen hankula tsakanin magoya bayan jam'iyyun adawa da 'yan takara daban-daban a waɗanann jihohi.
INEC ɗin ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan masu rura utar rikice-rikicen, tare da ɗaura ɗamara domin kawar da abubuwan da suka saɓa wa Dimkoraɗiyya a lokacin zaɓen kamar batun sayen ƙuri'a da kai wa ma'aikatan zaɓen hari tare da kawo cikas ga harkokin zaɓen.
A ranar 11 ga watan Nuwamba ne dai za a gudanar da zaɓukan gwamnoni a jihohin uku.