Rundunar 'yansa jihar Bauchi ta ce ta kama wani mutum da take zargi da cire wa wani matashi hannu tare da sare masa kai.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Ahmed Wakili ya fitar, ya ce mutumin mai suna Muhammad Abdullahi na daga cikin jerin mutanen da rundanar 'yan sandan jihar ke neman ruwa-a-jallo kimanin shekara biyu da suka gabata kan zargin aikata daba tare da munanan ayyuka.
SP Wakili ya ce mutumin ya aikata laifin tare da wasu mutum biyu da rundunar ke ci gaba da nema.
Sanarwar ta ce an kama Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Luwawu ne, a lokacin da tawagar 'yan sanda suka kai samame gidansa da ke birnin Bauchi.
“Tun shekarar 2021 rundunar 'yan sandan Bauchi ke nemansa ruwa-a-jallo kan zargin haÉ—in baki wajen aikata miyagun laifuka da suka haÉ—ar da daba, da ji wa mutanen raunuka da cutar da su, da sauran munanan laifuka'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa a shekarar 2021 ne Muhammad Abdullahi tare da haɗin bakin wasu mutum biyu ɗauke da adduna da sauran miyagun makamai suka sari wani mutum mai suna Mubarak Abdullahi da wuƙa a kansa tare da fille masa tafin hannunsa''.
SP Wakili ya kuma ce mutumin da ake zargi ya amsa laifin a lokacin da aka tuhume shi da aikata lafin.
Ya ƙara da cewa rundunar na ƙoƙari domin kamo sauran mutanen da ake zargi da aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kotu.