Kotun ta yanke hukunci da cewa dakatar Emefiele ya ci gaba da zama a gidan yari na Ikoyi da ke Legas har sai ya cika belin da aka ba shi a kan naira miliyan 20.
Jami’an DSS sun matsa kaimi wajen sake kama Mista Emefiele bayan shari’ar kotun da ta kai ga yin kace-nace tsakanin jami’an tsaron biyu.
An tuhumi Emefiele da laifin mallakar bindiga da harsasai daga hukumar DSS ba bisa ka'ida ba. Zargin da ya musanta.
Mai Shari’a Nicholas Oweibo ne ya bayar da belin Emefiele, mai shekaru 61, wanda ya yi watsi da ikirarin da gwamnati ta yi na cewa zai iya tserewa zuwa wani Æ™asa idan ya sami sarari.
An dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba