An gurfanar da gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da aka dakatar, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas a safiyar Talata bisa zargin aikata laifuka biyu da suka hada da mallakar makamai da alburusai ba bisa ka'ida ba.
An gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo, bayan shafe sama da makonni shida da kama shi da hukumar DSS ta yi.
Bayan fafutuka da lauyan Emefiele ya yi na kalubalantar tsare shi na tsawon lokaci da hukumar DSS ke yi, ‘yan sandan sirrin suka gurfanar da shi a gaban kotu a ranar 13 ga watan yuli saboda da matsin lamba da ke kansu.
Da ya bayyana a gaban mai shari’a Oweibo, Emefiele ya ƙi amsa laifin da gwamnati ke tuhumarsa da shi.
Tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Joseph Daudu ne ya jagoranci sauran lauyoyin da ke kare Emefiele.
Shugaba Bola Tinubu dai ya dakatar da Emefiele a matsayin shugaban babban bankin Najeriya ne a ranar 9 ga watan Yuni, 2023. Kwana daya bayan haka, hukumar DSS ta tabbatar da cewa ta kama Emefiele.
A yanzu haka an bada belin Emefiele kan nera miliyan 20.