An kama matashiyar ne a makon da ya gabata kan zargin nuna rashin ɗa'a ga Annabi Muhammad (S.A.W)
Idan dai aka same ta da laifi, za ta fuskanci hukuncin kisa ba tare da tanadin ɗaukaka ƙara ba.
Mauritania ta ƙarfafa tanadin hukunci kan laifin saɓo a ƙasar a shekarun nan, inda ta soke tanadin tsallake hukuncin kisa ga wanda ya nuna nadama bayan an kama shi da laifin aikata saɓo.
Amma duk hakan, shekara 30 kenan ba a taɓa zartar da hukuncin kisa ba a ƙasar.
Kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito cewa an kama ɗalubar ne a ranar 18 ga watan Yuli a garin Atar dake arewa maso yammacin ƙasar abisa zargin rashin mutumta Annabi da kuma amfani da kafar sada zumunta wajen cin mutumcin addinin Islama.
Babu dai cikakken bayani kan furucin da ta yi.
Daga baya dai iyalan ɗalubar sun fitar da wata sanarwa inda suka nemi gafara kan abin da ta aikata, sun kuma bayyana cewa tana fama da matsalar taɓin hankali.