Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da alamu ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya na iya aiwatar da umarnin kotu na hana kungiyoyin kwadagon shiga yajin aikin saboda janye tallafin man fetur a watan Mayu idan har kungiyar ta tabbatar da barazanar fara yajin aiki a ranar 2 ga watan Agusta.
Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya bayyana rokon da Tinubu ya yi ga menema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan da ya jagoranci wasu jami’an majalisar domin su yi wa shugaban kasa bayanin sakamakon zaman da suka yi da kungiyar Likitoci ta kasa, wadda ta shelanta yajin aikin a fadin kasar.
Abbas ya ce, Tinubu ya roki cewa kasancewar sa sabo a kan muƙamin, yana bukatar lokaci domin tantance batutuwan da ma’aikata suka gabatar a kai wanda har yanzu ba a yi masa bayani ba.
“Har yanzu Tinubu sabo ne a muƙaminsa. Mun roƙe su don Allah su ba shi lokaci kadan."
"Abubuwan da ƴan ƙungiyar suka ambata, bai san su ba, har yanzu ba a yi masa bayanin duk wadannan batutuwa ba."
"An karkatar da hankali ne sosai kan yadda za a hanzarta bin diddigin ayyukan da za su kawo taimako, musamman a kan jigilar jama'a, da rage tashin farashin sufuri."
A ranar Larabar da ta gabata ne ƙungiyar ƙwadago ta bayyana shirin fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai daga 2 ga watan Agustan 2023.