Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Godwill Akpabio ya tabbatar da cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayen mutum 28 da yake neman a tantance domin naɗawa a muƙaman minista.
Sunayen da shugaban majalisar ya karanta su ne:
- Abubakar Momoh
- Yusuf Maitama Tuggar
- Ahmad Dangiwa
- Hannatu Musawa
- Uche Nnaji
- Betta Edu
- Dr. Diris Anite Uzoka
- David Umahi
- Ezenwo Nyesom Wike
- Muhammed Badaru Abubakar
- Nasir El Rufai
- Ekerikpe Ekpo
- Nkiru Onyejiocha
- Olubunmi Ojo
- Stella Okotete
- Uju Kennedy Ohaneye
- Bello Muhammad Goronyo
- Dele Alake
- Lateef Fagbemi
- Mohammad Idris
- Olawale Edun
- Waheed Adebanwp
- Iman Suleman Ibrahim
- Prof Ali Pate
- Prof Joseph Usev
- Abubakar Kyari
- John Enoh
- Sani Abubakar Danladi
Babban dalilin da yasa ake ganin Tinibu bai tura da sunan wani daga kano ba shine : Akwai wanda suka cancanci muƙamin minista a kano daga jam'iyyar APC kuma suna da mabiya dai-dai gwargwado sai dai a wannan ƙadamin babu wanda zai yarda ya baiwa wanda bashi da faɗa aji a jihar sa kuma bashi da tarin ƴan dangwale, izuwa yanzu dai jam'iuyar APC nata turka-turka kan duba yiwuwar baiwa madugun siyasar Kano na Jam'iyyar NNPP Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso damar samun kujerar minista kasancewar ba ɗan jam'iyyar bane.

