Sabon shugaban ƙasar ya bayyana a kafar talabijin ta ƙasar, inda ya rinƙa zayyano matsalolin da ya ce ƙasar na fuskanta da suka kai su ga ɗaukan matakin kifar da gwamnatin Bazoum
Daga baya Janar Tchiani ya yi kira ga al'umma ƙasar su bai wa gwamnati haɗin kai ta yadda za a samu nasarar tafiyar da lamurran ƙasar cikin nasara.
A ranar Laraba ne Janar Tchiani ya jagoranci dakaru masu tsaron fadar gwamnatin ƙasar wajen tuntsurar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum.
Kuma har yanzu tsohon shugaban na hannun dakarun na Nijar.