Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci zaman a Abuja, babban birnin Najeriya.
Mista Tinubu dai shi ne sabon shugaban kungiyar Ecowas.
Cikin wata sanarwa, shugaba Tinubu ya yi Alla-wadai da juyin mulkin, inda kuma ya yi wa al'ummomin kasashen waje cewa zai yi duk mai yiwuwa domin kare dimokuraÉ—iyya da kuma tabbatar da É—orewar kyakkyawar shugabanci a yankin.