An yanke wa ɗan bindigar da ya hallaka mutum goma sha ɗaya a wani wajen ibadar Yahudawa a birnin Pittsburgh, na Amurka, hukuncin kisa.
Bayan waɗanda suka mutu, akwai mutum bakwai da suka haɗa da 'yan sanda biyar , waɗanda suka samu raunuka a lokacin da Robert Bowers ya buɗe wuta a wajen ibadar na Tree of Life,shekara biyar da ta wuce.
Bakin dukkanin masu taimaka wa alkali yanke hukunci, na tarayya ya zo ɗaya cewa a zartar masa da hukuncin kisa.
Kuma masu gabatar da ƙara sun kafe cewa mutumin ya tsani Yahudawa, kuma bai nuna nadama ba a kan harin.
Yayin da su kuwa lauyoyinsa suka ce yana da matsalar kwakwalwa sosai, a don haka suka bukaci a yanke masa hukuncin ɗaurin na rai da rai, ba tare da damar yi masa afuwa ba nan gaba.
Wannan shi ne hukuncin kisa na farko na tarayya a Amurka, ƙarƙashin gwamnatin Biden.