Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya baiwa ƴan ƙasar tabbacin cewa baza a ƙara farashin man fetur ba.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale, wanda ya bayar da tabbacin yace a yanzu babu shirin ƙara farashin man fetir ɗin.
“A ranar talata da safe na samu ganawa da Shugaba Tinubu. Mun tattauna kan abubuwan da ke faruwa a ƙasa game da man fetir," a cewarsa.
“Shugaban ƙasa yana jaddada matsayar kamfanin mai na ƙasa NNPCL cewa ba za a ƙara farashin man fetir ba yanzu. Muna ƙara jaddada hakan.''
Kakakin ƙungiyar dillalan man fetir ta Najeriya Chief Chinedu Ukadike ne ya fara tsegunta batun ƙarin farashin man, inda ya ce ƴan Najeriya su tsammaci tashin farashin mai saboda rashin daidaiton darajar naira a kasuwar canjin kuɗi.
Lamarin ya haifar da ruɗani tsakanin jama'ar ƙasar, har ya kai ga ƙungiyoyin ƙwadago sun yi barazanar shiga zanga-zanga.