Ƙungiyar Masana Na'ura mai ƙwaƙwalwa ta ƙasa NSC reshen jihar kano, da Ƙungiyar haɗaka ta ƙwararru na kowane bangare wato Association of Professional Bodies sun gudanar da babban taro a Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma wato CITAD inda aka tattauna batu kan yadda za'a ƙirƙiro da sabbin hanyoyin bunƙasa ilimin nazarin na'ura tun daga fari da kuma bada dukkannin gudunmawa ta kayayyakin aiki da koyar da ilimin a hanyoyi masu sauƙi ta yadda za'a fahimtar da matasa mata abunda ake nufi da ilimin nazarin na'aura mai ƙwaƙwalwa wanda a gefe guda hakan zai samarwa da Matasa aikin yi domin dogaro da kai.
Yayin jawabin sa Shugaban Ƙungiyar ta NSC Engr. Lukhman wanda ya samu wakilcin Ma'ajin Ƙungiyar Engr. Balarabe Umar Waziri ya bayyana cewa burin su a kullum shine yadda za'a cusawa yara masu tasowa ilimin nazarin na'ura mai ƙwaƙwalwa tun daga fari.......
Ka Zaluka Engr. Rabi'u Haruna wanda ke zama jigo a babbar Ƙungiyar haɗaka ta ƙwararru na kowane bangare a jihar kano yace da yiwuwar haƙan su zai cimma ruwa wajen ganin matasa sun samu ilimin nazarin na'ura mai ƙwaƙwalwa musamman duba da yadda CITAD tayi alƙawarin goyon bayan ƙudurin nasu koda yaushe domin samun aikin yi don dogaro da kai...
A ƙarshe shugaban Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma Engr. INUSA YA'U ZAKARI yace wannan al'amari zai haifar da Ɗa mai ido da kuma jaddada baiwa waɗannan ƙungiyoyi haɗin kai na gudunmawa ƙarƙashin wannan cibiya ta CITAD.