Guda cikin wadanda rundunar yan sandan jihar Kano ke nema ruwa a jallo, Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Chile Maidoki daga layin Falwaya a Kurna, ya kawo kansa, ya kuma tuba tare da nadama.
Rundunar na ƙara sanar da al'umma dangane da farautar Abba Burakita Dorayi, da Kuma Hantar Daba Kwanar Diso.