Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bukaci hadin kai da goyon bayan Buritaniya domin inganta Ilimi da kiwon lafiya.
Gwamnan ya bayyana bukatar hakan ne yayin da ya karbi bakuncin sabon jakadan Britaniya Mr Richard Montgomery Wanda ya kawo masa ziyara a gidan gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya lissafa sauran bangarorin da gwamnatin jihar Kano take bukatar tallafin burtaniya da suka hada da noma da magance matsalar dumamar yanayi da tallafawa ilimin 'yaya mata da kananan Yara da Kuma masu bukata ta musamman.
Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda ya bayyana doguwar dangantakar dake tsakanin Kano da Britaniya, ya Kuma bayyana godiyarsa bisa gagarumar gudummar da Britaniya take bawa kasar nan ta fuskoki da dama karkashin kungiyar raya kasashe rainon Ingila.
Ya bukaci Britaniya ta kara zuba hannun jari a jihar Kano Kasancewar jihar na bukatar masu zuba hannayen jari daga kasashen ketare.
Ya taya sabon jakadan murna tare da fatan zai ci gaba da kulla dangantaka mai Karfi tsakanin Burtaniya da jihar Kano.
Da yake jawabi tun da farko Mr. Richard Montgomery yace ya kawo ziyara fadar gwamnatin jihar Kano ne domin tattaunawa kan bangarorin da zasu yi hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano.
Ya bada tabbacin Burtaniya zata tallafawa jihar Kano a bangaren ilimi da kiwon lafiya da nowa da sauran al'amuran cigan Al’umma.