Jirgin saman yana kan hanyarsa ta zuwa jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar lokacin da ya yi hatsarin a yau Litinin.
Kakakin rundunar sojin, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce jirgin ya faɗi ne a wani ƙauye da ke cikin ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
“Jirgin rundunar sojin saman Najeriya mai lamba MI-171 ya yi hatsari a kan hanyarsa ta kai ɗauki a yau, 14 ga watan Agustan 2023, da misalin ƙarfe 1:00 na rana agogon Najeriya a ƙauyen Chukuba na jihar Neja," a cewar sanarwar.
“Jirgin ya tashi ne daga makarantar firamaren Zungeru da niyyar zuwa Kaduna amma daga baya aka gano ya yi hatsari a kusa da Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro.”
Gabkwet ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ceto matuƙin jirgin da sauran fasinjojin da ke cikinsa.
Lamarin ya faru ne wata biyu bayan wani jirgin koyarwa na sojin Najeriyar ya faɗo a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai - ita ma a arewa ta tsakiyar ƙasar.