Mahukunta a Amurka sun tabbatar da cewa an damƙa musu wasu ƴan Najeriya biyu da kotu ta kama da laifukan da suka jiɓanci amfani da hotunan batsa ta intanet don zambatar mutane kuɗi.
An kama mutanen ne a Najeriya, sannan aka tasa ƙeyarsu zuwa Amurka ta hanyar haɗin-gwiwar jami`an tsaro na ƙasa da ƙasa da hukumomin Amurka da Najeriya.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka ya fitar ta ruwaito lauyan gwamnatin Amurka mai gabatar da ƙara na gundumar Michigan, Mark Totten, yana cewa Samuel Ogoshi, ɗan shekara 22 da kuma Samson Ogoshi mai shekara 20, mazauna jihar Legas ne sun isa Amurka domin gurfana a gaban kotu, bayan an kama su da aikata wasu laifuka huɗu.
Laifukan da ake zargin su da aikatawa sun haɗa da aikata batsa ta intanet, inda suke tattara hotunan tsiraici daga wasu matasa fiye da 100 kuma su yi amfani da su wajen yin barazanar bankaɗa ko tonon asiri ga masu hotunan idan ba su ba su wani adadin kuɗi ba.
Samuel Ogoshi da Samson Ogoshi duka suna yaudarar mutane ne ta intanet a matsayin mata. Kuma sukan sayi shafukan intanet na wasu ne da aka yi.
Wadanda ake tuhumar kan yi amfani da wasu manhajoji na intanet wajen tattara bayanai a kan makarantu da abokai da dangin matasan da suke yaudara, sai su nuna musu cewa sun san abokansu, don haka za su tura musu hotunan tsiraicin idan ba su ba da hadin kai ba.
Kazalika ana tuhumar Samuel Ogoshi da yin sanadin mutuwar Jordan Demay, wani dan shekara shekara 17 da haihuwa da ke Makette, wanda aka tsinci gawarsa da alamar ya harbe kan sa a watan Maris din bara.
Lauyan gwamnatin Amurka, Mark Totten ya ce an yi nasarar kama mutum biyun tare da iza keyarsu zuwa Amurka cikin gajeren lokaci ne sakamakon hadin-gwiwar da ke tsakanin hukumar da ke binciken manyan laifuka ta Amurka da jami'an tsaron Najeriya.
A yau Litinin ake sa ran za a kai waɗanda ake tuhumar gaban shari'a