Hukumomi sun ce fim ɗin da aka fitar a watan da ya gabata, ya saɓa wa kyawawan ɗabi'un Aljeriya.
Kamfanin dillancin labarai na reuters ya ruwaito wata majiyar hukuma tana cewa fim ɗin yana tallata harkan neman jinsi da kuma rashin tarbiya na ƙasashen yamma, kuma "bai dace da akidar addini da al'adun Aljeriya ba".
Kuɗin da aka samu daga sakin fim ɗin a ranar 21 ga watan Yuli, ya zarce dala biliyan ɗaya.
Wasu ƙasashe da suka haɗa da Lebanon da Kuwait sun hana fim ɗin saboda gurɓata tarbiya.