Kwamishinan ƴan sanda a jihar Usaini Gumel, shi ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce kalaman ɓatanci da mutanen suka yi sarkin, za su iya tayar da hargitsi.
Ya kwatanta waɗanda suka yi kalaman da cewa masu zagon ƙasa ne da kuma makiyan jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamishinan ƴan sandan na cewa lamarin ya kusa hargitsa bikin sake buɗe asibitin, inda ta ce tuni ma ta gano mutane shida cikin waɗanda suka yi kalaman.