Ƙungiyar kare fararen hula da ke sanya ido kan ci gaban dimokaraɗiya a Najeriya ta 'Transition Monitoring Group'(TMG)tan bayyana damuwarta kan yadda wasu da ta bayyana da 'marasa kishin ƙasa' ke son amfani da kuɗi don kawo tarnaƙi ga shari’un da ke gaban kotunan sauraron ƙararakin zaɓe a wasu daga cikin jihohin ƙasar.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce faruwar wannan al'amari abin takaici ne, adaidai lokacin da dimokradiyya ke fuskantar barazana a yankin yammacin Afirka, sakamakon ƙaruwar cin hanci da rashawa da wasu 'yan siyasa ke aiwatarwa.
Kungiyar ta kuma ƙara da cewa akwai buƙatar mayar da hankali domin tabbatar da cewa an kammala gudanar da shari'o'in ƙorafe-ƙorafen zaɓe cikin gaskiya da adalci.
A makon da ya gabata ne, shugabar kotun sauraron ƙorafin zaɓen 'yan majalisun tarayya da ta jihar Kano, Mai shari'a Flora Ngozi Azinge, ta sake fitowa ta koka game da yunƙurin bai wa alƙalan kotun cin hanci da nufin tauye adalci.
Ƙungiyar ta TMG ta ce iƙirarin Mai shari'a Azinge babbar damuwa ce ga duk wani mai kishin ƙasa.
Sanna kuma ƙungiyar ta yaba wa alkaliyar dangane da fitowa fili da ta yi tare da bayyana hakan.
Rahotanni dai sun ambato Mai shari'a Flora Azinge na cewa karo na biyu kenan wani alƙalin kotun na kai mata ƙorafi a kan yadda wasu lauyoyi da ke cikin ƙararrakin da kotun ke sauraro, suna ƙoƙarin ba su cin hanci.
Zargin na babbar alƙaliyar, na nuna tsananin rufewar idon 'yan siyasa, ta yadda wasu ke ƙoƙarin sayen nasarar da suka kasa samu ta halastacciyar hanya daga jama'ar da za su mulka.