Ana sanar da jama'a cewa kwamitin tantance sabbin ma'aikata da gwamnatin da ta shude ta ɗauka aiki kwanan nan kwamitin na gayyatar ma'aikatan da abin ya shafa kamar yadda aka tsara.
(1) Ma'aikatan HMB & SUBEB za a tantance su ta panel 1 a zauren taro, CSC ranar 21/08/2023 da karfe 10:00 na safe
(2) Ma'aikatan CSC, HOS & KSSSMB za a tantance su ta panel 2 a ranar 21/08/2023 a Ma'aikatar Muhalli da karfe 10:00 na safe
(3) Ma'aikatan LGA da suka fara daga karamar hukumar Tarauni za a tantance su ta panel 3 ranar 21/08/2023 a ofishin SSG da karfe 10:00 na safe.
An shawarci Ma’aikatan MDAs da abin ya shafa su zo tare da buɗaɗɗe da fayilolin sirri na ma’aikatan da abin ya shafa
Hakazalika, Jami’an Watsa Labarai da Jami’an Hulda da Jama’a na MDAS da abin ya shafa ya kamata su sake yada wannan sako.
Sa hannu; Sakataren kwamitin. Ta hanyar
Jami'in yada labarai
Ofishin majalisar ministoci.
M.T. Muhammad