Baby M, wacce take son abincin Indiya kuma ta nuna tana cikin farin ciki a wani faifan bidiyo tare da iyayenta, yanzu tana zaune a wata cibiya na yara masu bukata ta musamman kusa da Berlin, a cewar mahaifiyarta.
Takaddamar dai ta fara ne a watan Satumbar 2021, lokacin da aka cire Baby M, mai watanni bakwai kacal daga kulawar iyayenta sakamakon zargin cin zarafin yara a kan ta.
Hukuncin da wata kotu ta yanke a birnin Berlin na baya-bayan nan ya kara tada jijiyoyin wuya yayin da aka dakatar da hakkin iyayen Dia da mijinta Amit (Ba ayi amfani da ainihin sunayen su ba saboda dalilai na shari'a) daga kula da yarinyar su, kuma aka mayar da kula da tsaron ta zuwa ofishin kulawan matasa na Jamus, Jugendamt.
Kotun ta sake kin amincewa da bukatar iyayen kan mayar da Baby M kasar Indiya.
Wannan hukuncin dai ya haifar da fusata, lamarin da ya sa iyayen suka kira shari’ar a matsayin “shari'ar karya” suka kuma shigar da kara.
Dia, wacce a halin yanzu tana Delhi don neman goyon baya ga manufarta na dawo da 'yarta Indiya ta bayyana bakin cikin ta da zafin rabuwa da 'yar ta da take Tattaunawa da BBC.
Dia da iyalin ta sun fara zuwa Berlin ne a cikin shekarar 2018, lokacin da Amit ya sami aiki a birni kasar. An kuma haifi Baby M a ranar 2 ga watan Fabrairun 2021.
A tsakiyar takaddamar, wani lamari da ya ja hankalin wani likita lokacin da Baby M tana da wata bakwai shine wani babbar raunin a kan al'aurar ta wanda hakan ya haifar da zargin cin zarafi da lalata, amma iyayen sun musanta hakan.
Kwararrun likitocin da suka duba raunin, daya daga cikin su ya bayyana raunin a matsayin abin da ba a taba ganin irinsa ba ga jariri kuma ya ce da dukkan alama sai anyi mata tiyata.
Wannan zargin na cin zarafi da lalata ne ya sa hukumar kare hakkin yara suka dauke ta suka wuce da ita.
Asibitin da aka kai yarinyar ba su gano wani shaida da ya tabbatar cin zarafi ne da lalata aka yi ma 'ya yarinyar ba, hakan ya sa ba a kame iyayen ba kuma polisawa suka rufe zancen.
Su dai iyayen sun ce raunin killa ya faruwa sakamakon wani hatsari ko wani abu dai, inda har wasu likitoci biyu daga Amurka da Indiya suka tabbatar da iyayen gaskiya suke fadi bayan ganin rahoton asibitin.
"Rauni mai yuwuwa ya faru ne sakamakon wani hatsari. Ba zai yiwu iyaye su raunata 'yar su ba da gangan sannan kuma suka garzaya da ita asibiti," in ji wani rahoto da aka mika a kotu.
Sai dai hukumomin kare yara sun ce ba sa tunanin Baby M za ta kasance cikin koshin lafiya a gida - takaddamar da kotun ta amince da shi.
Don haka, yanzu Babay M ta shafe kusan shekaru biyu a karkashin renon wasu daban na dan lokaci kuma iyayenta sun ce ba a wani basu dama da izinin ganin ta ba ko tuntubar sosai ba duk da cewa ma'aikatan kula da jama'a da aka sanya suna saka wa iyayen ido sun kwatanta su a matsayin iyaye masu "ƙauna da kulawa" tare da bayyana mu'amalar Babay M da su a matsayin "daidaitacce da kuma abin ban sha'awa".
Wani masanin ilimin halayyar dan adam da kotu ta nada ya kuma ba da shawarar cewa daya daga cikin iyayen ya zauna tare da Baby M a cikin cibiyar iyaye da yara wanda wanda ke karkashi kulawa mai kyau.
Amma a makon da ya gabata, ofishin kulawan matasa na Jamus, Jugendamt ta sanar da iyayen cewa "an soke duk wata damar ziyarar 'yar tasu da aka bayar in ji Dia, tana mai zargin cewa ba a ma bar su da su kira ta ta bidiyo ba a waya.
"Ba mu da wani bayani kan wanda ke kula da ita tun lokacin da aka dauke ta daga renon wadanda aka ba wa dama na dan karamin lokaci zuwa cibiyar kula da yara masu bukata ta musamman. Sirrin da ke tattare da 'yar namu abu ne mai ban mamaki."
Dia ta zargi hukumomin Jamus da "kwace mata yarinya saboda bambancin al'adu da kuma rashin fahimtar juna" - ta ce ba ta iya jin Jamusanci kuma mafassaran da aka ba ta yana ji yaran Hindi amma ba san yaran Gujarati ba. BBC ta tuntubi Jugendamt kuma ana jiran amsarsu.
Lamarin Baby M ta dauki hankula sosai a Indiya da Jamus -inda aka gudanar da zanga-zanga a biranen Indiya da dama da kuma 'yan Indiya mazauna Frankfurt da Darmstadt kuma an ba da tallafi ga iyayen.
A Delhi, Dia ta hadu da jami'ai daga ma'aikatar harkokin waje ta Indiya (MEA) da 'yan majalisa da dama inda har suka aika da wasika ga jakadan Jamus Phillip Ackerman kan mayar da Babay M zuwa Indiya.
Wani dan majalisar ya bukaci gwamnati da ta dauki matakan da suka dace domin dawo da ita. Wani dan siyasa kuma ya nemi Firayim Minista Narendra Modi da ya tuntubi shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz lokacin da zai ziyarci Delhi a watan gobe don taron G-20.
Ita ma Dia a yanzu ta roki Firayim Minista da ya sa baki. "Abin da nake fata yanzu shine firayim minista Modi ya sa baki kan lamarin, idan yayi hakan, 'yata za ta iya dawowa," in ji ta.
Surayya Aiyar, tsohuwar lauya kuma mai fafutuka wacce ta taimaka wa dangin Indiyawa a Norway kuma yanzu tana taimakawa iyayen Baby M, ta ce irin wannan lamari ba bakon abu bane.
"Wannan matsala ce mai mahimmanci wanda zato da zargi ne kawai ke hadasa irin hakan.
Majalisar Tarayyar Turai ma ta soki rawar da Jugendamt ke takawa a rikicin da lamarin. A cikin wani rahoto mai zafi da aka yi a cikin 2018, vTarayyar Turai ta zargi kungiyar da nuna wariya, rashin adalci ga yaran bakin haure, da kuma cutar da hakkin iyaye da yaran da suka kwace.
A cikin wani sabon rahoto da aka fitar a watan Mayu, Tarayyar Turai ta ce har yanzu kwamitinta kan kararraki yana samun korafe-korafe game da Jugendamt.
Ms Aiyar ta ce, mafi kyawun mafita a irin waÉ—annan yanayi, shine jihar ta ba da ma'aikatan lura da jama'a don taimakawa iyalai su kula da 'ya'yansu.
A lamarin Baby M kuma, tace mafita ita ce gwamnati ta shigo cikin harkan.
"Babu wani laifi da 'ya yarinyar ta yi, a bar ta kawai ta koma Indiya, 'yar Indiya ce kuma tana da haƙƙin zama a can."
Gwamnatin Indiya ta ce ana ba wa shari’ar fifiko sosai. Kakakin MEA, Arindam Bagchi ya fada a farkon wannan watan cewa "sun kira jakadan Jamus" don isar da damuwar Indiya a kan lamarin.
"A takaice dai mun yi imani ana tauye hakkin wannan yarinya a matsayinta 'yar Indiya," in ji Mista Bagchi a wani taron manema labarai.
Ya kara da cewa "Mun nemi a dawo da ita Indiya da wuri kuma za mu ci gaba da matsawa Jamus lamba kan wannan batu.
Kakakin ofishin jakadancin Jamus a Delhi ya ki cewa komai kan lamarin. Sai dai wasu majiyoyin gwamnati a Jamus sun ce shari'ar tana gaban kotu kuma ba ta hannunsu, inda suka kara da cewa suna aiki tare da Indiya don ganin an shawo kan lamarin.
Hukumomin Indiya sun ce sun gano wani iyali a Gujarat - jihar da ke yammacin Indiya inda iyayen suka fito - sun ce za a iya sanya Baby M a karkashin kulawar su.
Dokta Kiran Aggarwal, likitan yara na gwamnati wacce tayi ritaya kuma tsohuwar mamba a kwamitin kula da yara na gwamnatin Delhi, ta ce ya kamata Baby M ta kasance tare da iyayenta.
"Indiya tana da tsauraran dokokin kare yara kuma idan kotun Jamus ta mayar da ita, za a iya kula da ita a Indiya," in ji ta.
Yayin da lokaci ke wucewa, Dia ta ce kowace rana tana ƙara mata damuwar cewa za ta iya rasa 'yar ta.
"Ba ta iya koyon yaren mu na Gujarati, da Jamusanci kawai ake yi mata magana kuma yaran da ta iya kenan, ta yaya zan iya magana da ita?" Dia ta tambaya.
Iyayen kuma suna kokawa kan biyan rupees miliyan 9 (dala 108,477 kenan) da aka umarce su da su biya don kulawar 'yar da aka bai wa wasu da kuma kuÉ—in kotu.
"Mun tara kudi ta hanyar tattara kudade kuma mun riga mun biya rupees miliyan 5. Mu masu matsakaicin samu ne. Abin nan da ke faruwa ta taba lafiyar mu da tunanin mu, yanzu kuma suna kokarin karya mu" inji ta
BBC