Jaridar Premium Times ta ruwaito shugaban kwamiin, Ademorin Kuye a cikin wata sanarwa yana cewa za su binciki yadda aka sayar da helikwaftan ƙirar Bell 206L-3 wanda aka sayo da dukiyar al'umma.
Ya ce gwamnati ta sayar da jirgin ne a daidai lokacin da rundunar sojin ruwa take buƙatar irinsa don inganta ayyukanta.
“Kwamitinmu zai binciki yadda aka sayar da wannan kadara ta gwamnati mai amfani sosai wajen horas da matuÆ™a jirgin sama, don tabbatar da cewa an bi Æ™a'ida kuma ba a cuci Æ™asarmu a cinikin ba” in ji Ademorin Kuye.
A ranar Alhamis da ta gabata ne, kakakin majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya ƙaddamar da kwamitocin majalisar, kafin sanar da tafiya hutu.