Ƙungiyar ƙasashen ta kira taron ne bayan wa'adin da ta bai wa shugabannin mulkin sojan Nijar na cewa su mayar da mulki hannun hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed ya cika a ƙarshen makon jiya.
Kawo yanzu Shugabannin Saliyo da Guinea Bissau sun isa Abuja a shirye-shiryen wannan taro.
Ga wasu hotuna na zauren da za a gudanar da taro: