Gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu na kano wato (Kano Civil Society Organization) sun koka kan ya suka bayyana cewa wasu a cikin su na ƙoƙarin tada zaunae tsaye duba da ƙaratowar zabe da za'a ayi kwanaki kaɗan masu gabatowa a cikin ƙungiyar.
Gamayyar ƙungiyoyin sun bayyana hakan ne jim kaɗan da wata jarida ta Online ta wallafa zantuka marasa daɗi wanda ƙungiyar ta kwatantasu da zancen ƙanzon kurege wanda bashi da tushe balle makama.
Wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sun bayyana cewa wasu matsorata sojojin haya wanda suke kiran kansu kungiyoyin fararar hula sune suka ɗaura ɗamarar haddasa fitina a cikin su kuma sun ƙara da cewa babu wata rigima dake a tsakanin su face haɗin kai da son juna haɗi da girmama junan su.